'Na san Ferguson zai bar Man U'

Image caption Mourinho ya ce ya gwammace ya koma Chelsea

Kocin Chelsea, Jose Mourinho, ya yi ikirarin cewa tun watanni da dama da suka gabata ya sani cewa Sir Alex Ferguson na shirin barin Manchester United, amma bai yi tayin komawa kulob din ba saboda ya gwammace ya koma Chelsea.

Ferguson, mai shekaru 71 a duniya, ya yi murabus daga Manchester United ne a watan jiya bayan ya shafe shekaru 26 yana jagorancin kulob din.

Tuni dai aka maye gurbinsa da David Moyes.

A cewar Mourinho, "Ina sane cewa Ferguson zai ajiye aikinsa watanni da dama da suka wuce.Da a ce an nemi na zama kocin wata kasa a duniya, ciki har da Manchester United, da ba zan karba ba. Ni Chelsea kawai nake son komawa"

An dade ana alakanta Mourinho, mai shekaru 50 a duniya, da yunkurin maye gurbin Ferguson a United, sai dai ya jaddada cewa ba shi da sha'awar komawa kowanne kulob idan ba Chelsea ba - duk da cewa Ferguson ya shaida masa shirinsa na yin murabus.

Karin bayani