FIFA na binciken Ethiopia da Togo

Image caption FIFA ba ta fadi sunayen 'yan wasan da ba su cancanta ba

FIFA tana gudanar da bincike kan kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Ethiopia da Togo saboda zargin da aka yi cewa sun sanya 'yan wasan da ba su cancanta ba a wasannin cancatar shiga gasar cin kofin duniya.

Hakan dai zai iya sanyawa Ethiopia ta rasa gurbi a wasan kusa da na karshe a cancantar shiga gasar cin kofin wacce za a yi a kasar Brazil a shekarar 2014.

Hukunta kungoyoyin kwallon kafa na kasashen biyu zai iya yin tasiri a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da kasashen Afirka ke yi, amma kuma zai iya taimakawa kasashen Afirka ta kudu da Kamaru su samu shiga gasar yayin da zai kawo nakasu ga Libya.

A ranar Lahadi ne Ethiopia ta yi nasarar zuwa wasan karshe na cancantar shiga gasar a watan Oktoba da Nuwamba inda ta doke Afirka ta kudu da ci 2 da 1, amma tana fuskantar kwace nasarar da ta yi a wasan da ta buga da Botswana, wanda suka tashi da ci 2 da 2 a watan Yuni saboda zargin da ake yi mata cewa ta sanya dan wasan da bai dace ba.

FIFA ta kara da cewa tana gudanar da bincike kan kwallon da Togo ta buga da Kamaru inda ta ci Kamaru 2 babu ko daya, tana mai cewa mai yiwuwa ta bai wa Kamaru kwallayen da Togo ta ci, lamarin da zai sanya ta dara Libya a wajen buga wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

FIFA ba ta ambaci sunayen 'yan wasan da ta ce ba su cancanta ba da kuma dalilan rashin cancantarsu.

Karin bayani