Ban yi shirin zama koci ba —Owen

Image caption Owen ya ce ba ya gaggawar zama koci

Michael Owen ya ce ba ya gaggawar bin sahun tsohon abokinsa Paul Ince don zama koci.

Owen ya daina taka leda a watan jiya bayan ya yi wasa a kulob-kulob da suka hada da Liverpool da Real Madrid da Newcastle United da Manchester United da kuma Stoke City.

Tsohon dan wasan na Ingila ya zura kwallaye fiye da dari 200, lamarin da ya sanya ake daukarsa a matsayin daya daga cikin kwararrun 'yan wasa a zamaninsa.

A yayin da wadansu daga cikin abokan wasan Owen da suka hada da kocin Blackpool, Ince suka zama masu horar da 'yan wasa bayan yin murabus daga wasa, shi kuwa Owen ya ce zai yi nazari yayin da yake son mayar da hankali kan wani kamfani da yake muradin budewa don yi wa kananan 'yan wasa jagaba a harkokinsu.

Karin bayani