West Ham na gwada lafiyar Carroll

Image caption West Ham sun ce suna yi wa Carroll gwaji sosai

West Ham na gwada lafiyar dan wasan gaba na Liverpool Andy Carroll gabanin sayensa da za su yi a kan kudi pam miliyan goma sha biyar.

Liverpool ta sayi dan wasan mai shekaru 24 a duniya a kan pan miliyan 35, kuma ta ba wa West Ham aronsa tun shekarar 2012, inda ya zura kwallaye bakwai a wasanni 24 da ya buga.

A watan Mayu aka amince a kan kudin da za a saye shi sai dai dan wasan yana tababa a kan komawa kungiyar shekara guda kafin gasar cin kofin duniya.

Za a gudanar da binciken kwa-kwaf a kan koshin lafiyar Carroll ganin cewa za a saye shi da tsada, da kuma yin la'akari da raunukan da ya samu, don haka watakila sai ranar Laraba za a kammala batun sayen nasa.

Karin bayani