Kotu na tuhumar Ribery da Benzema

Ribery da Benzema
Image caption Ribery da Benzema

Biyu daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa na Faransa, Franck Ribery da Karim Benzema za su gurfana a gaban kuliya.

Ana zargin 'yan wasan biyo da lalata da 'yan matan da ba su kai shekaru 18 ba.

Dan wasan kulob din Bayern Munich, Ribery ya amince cewa ya yi lalata da Zahia Dahar, a lokacin tana da shekaru 16 a duniya.

Sai dai ya ce bai san ainihin shekarunta ba.

Yayin da dan wasan kulob din Real Madrid, Benzema ya musanta zargin yin lalatar.

Dahar wacce a yanzu ke da shekaru 21, kuma ta mallaki kamfanin yin kamfai da sauran kayan mata, ta amince cewa ta yi karya game da shekarunta.

Sai dai mai shari'ar ya yi watsi da hakan, yana mai cewa babu yadda za su kasa ganin cewa akwai kuruciya a tare da ita.

Idan an same su da laifi, za a yanke musu hukuncin shekaru uku a gidan yari.