Newcastle ta tabbatar da nadin Kinnear

Sabon daraktan Newcastle Joe kinnear
Image caption Sabon daraktan Newcastle Joe kinnear

Newcastle ta tabbatar da nadin Joe Kinnear a matsayin daraktan kwallon kafar kulob din na tsawon shekaru uku.

Kulob din ya fitar da sanarwar ce bayan da tsohon manajansu 'Magpies' ya sanar da cewar shi ma zai dauki ayyukan kulob din.

Kinnear dan shekaru 66 zai yi aiki da hukumar da ke kula da kulob din a matsayin babban jami'i mai kula da abubuwan da suka shafi kwallon kafa a dandalin St James.

Kocin Newcastle Alan Pardew zai yi aiki a karkashin Kinnear.

Manajan darakta, Derek Llambias ya sanya a shafin kulob din na yanar gizo cewa hukumar na farin cikin dawowar Joe cikin kulob din Newcastle.

Ya kara da cewa ''Joe kwararre ne a sha'anin kwallon kafa, kuma wannan kwarewar tasa abu ne da kulob din mu zai amfana da shi don cimma abinda muke fata a kakar wasanni ta gaba.''

Sabon jagoran kulob din Newcastle zai yi aiki da Kinnear, cikin sabon garanbawul din da aka yi wa kulob din bayan kalubalen da suka fuskanta a kakar wasannin da ta gabata, inda aka kare Newcastle na ta biyar a kasan teburin Premier League.

Kinnear shi ne manajan kulob din na Newcastle a tsakanin watan Satumbar shekarar 2008 zuwa Fabrairun 2009, kafin wa'adin aikin sa ya kare, a lokacin da ya ke fama da ciwon zuciya.