Reid ya sanya hannu a kwantiragi

Image caption 'Yan wasan WestBrom na taka leda

Dan wasan baya na West Brom, Steven Reid, ya sanya hannu a wani sabon kwantiragi na shekara daya da kulob din.

Jami'an West Brom sun fara tattaunawa da dan wasan mai shekaru 32 a duniya ne bayan ya gaza buga adadin wasannin da za su kai ga tsawaita kwantiraginsa na baya.

Kocin kulob din, Steve Clarke, ya shaidawa shafin intanet na kulob din cewa, "Idan ya ji saukin raunukan da yake fama da su, Steven zai samu babbar dama ta buga wasa a kulob din a kakar wasa ta bana''.

Reid ya je West Brom ne a matsayin aro na watanni daga Blackburn shekaru uku da suka wuce, amma daga bisani ya sanya hannu don bugawa kulob din wasanni.

Karin bayani