Mohammed ya lashe zaben hukumar kwallon Kamaru

Iya Mohammed
Image caption Akwai yiwuwar bangaren da suka sha kaye a zaben su kalubalanci zaben Mohamed

An sake zaben shugaban hukumar kwalllon kafa na Kamaru, Iya Mohammed domin sake shugabantar hukumar a karo na biyu.

Hakan ya faru duk da cewa Mohammed na tsare a hannun hukumomin kasar.

A ranar 10 ga watan Yunin da muke ciki ne aka kama Mohammed, bisa zargin dake da alaka da mukaminsa na shugaban kamfanin auduga na kasar.

Ya samu nasarar lashe zaben da aka yi ranar Laraba bayan wani dan jinkiri, a lokacin da 'yan sanda suka hana wakilai shiga shalkwatar hukumar wasan domin kada kuri'a.

Mataimakinsa Mbombo Njoya ne zai ci gaba da jan ragamar hukumar, kafin lokacin da za a sake shi,.

Tun da fari dai hukumomin Kamaru sun dakatar da zaben, sai dai hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta sanya baki a lamarin.

Inda ta yi barazanar dakatar da kasar daga shiga gasar kasa da kasa, idan har gwamnati bata daina tsoma baki a sha'anin kwallon kafa na kasar ba.

Sai dai tana kasa tana dabo, domin da yawu daya wakilan sun kada kuri'ar yin fatali da wata yarjejeniya da aka cimma na sasanta hukumar kwallon kafar da gwamnati.

Kuma hukumar FIFA ce ta sa ido aka cimma yarjejeniyar.