Spain na tuhumar Messi kan haraji

Image caption Messi na fuskantar tuhumar haraji

Hukumomin kasar Spaniya sun tuhumi babban dan wasan Kulob din Barcelona Lionel Messi da laifin kin biyan haraji.

Dan wasan zai gurfana a gaban kuliya a watan Satumba mai zuwa.

Messi, dan asalin kasar Argentina da mahaifinsa na fuskantar tuhumar kin biyan harajin da ya zarta dala miliyan biyar.

Sai dai ya musanta aikata laifin.

Idan an same shi da laifi, akwai yiwuwar a yanke wa Messi hukuncin daurin shekaru shida a jarum.

Karin bayani