Liverpool ta sayi Alberto

Image caption Liverpoll ta ce Alberto ya iya taka-leda

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sayi dan wasan gaba na Sevilla, Luis Alberto, a kan kusan pam miliyan bakwai.

Kungiyar Barcelona B ce ta yi aron dan wasan mai shekaru 20 a duniya, sai dai ba ta nuna sha'awar sayensa ba shi yasa ma Liverpool ta nuna sha'awar sayensa.

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce, " Luis Alberto ya iya taka-leda kuma yana da nutsuwa da za ta sanya ya zama dan wasan Liverpool. Ina sa ran aiki da shi domin karfafa masa gwiwa kan yadda zai rika taka-leda''.

Alberto ya fara buga wasa ne a lokacin yana dan shekaru 18 a watan Afrilun shekarar 2011.

Ya bugawa Barcelona B wasa sau 38 a kakar wasa ta bara, inda ya zuwa kwallaye 11.

Karin bayani