Tottenham ta nemi Paulinho

Image caption Paulinho na shawara kan komawa Tottenham

Dan tsakiyar nan na Brazil, Paulinho, ya bayyana cewa Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta nuna sha'awar daukar sa amma ba zai iya yanke hukunci ba sai bayan gasar cin kofin Nahiyoyi.

Dan wasan ya ce kamar yadda ya yi ga Inter Milan, " zan zauna da iyalina mu yi shawara kafin na yanke duk wani hukunci".

Paulinho, bai buga wasan ranar Asabar ba saboda raunin da ya yi a idon sawu.

Dan wasan ya bugawa Brazil wasanni 15 kuma ya ci sau hudu har da kwallon da ya ci a wasan da suka lallasa kasar Japan da ci uku ba ko daya a gasar cin kofin Nahiyoyi.

Karin bayani