Shin ko Ghana da Najeriya za su yi azama?

Image caption Ghana da Najeriya ko za su yi azama?

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Ghana da Najeriya za su yi fatan su kara azama a wasanninsu na gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 20 bayan da aka lallasa su a wasannin farko da suka yi.

Kasar Faransa dai ta ci Ghana uku da daya, cin da ba a taba yi musu irin sa a ba a zagaye na rukuni-rukuni ba.

Najeriya kuwa Portugal ce ta ci ta uku da biyu.

Mai ba da horo na Ghana, Sellas Tetteh, ya dora alhakin nasarar da aka yi akansu da irin salon wasan da suka buga na tsaron gida.

Shi kuwa takwaransa na Najeriya, John Obuh, cewa ya yi wasa ne da aka yi gumurzu amma rashin sa'a ne ya sa aka ci su kodayake ba haka suka so ba.

Karin bayani