Italiya ta hana 'yan wasa bin tituna

Image caption Italiya na kokarin kare lafiyar 'yan wasanta

Kasar Italiya ta hana 'yan wasanta barin wajan kwanansu a Salvador don kare lafiyar su.

Kodayake mai bada horo na tawagar Cesare Prandelli, ya bar Mario Balotelli ya fita saboda bakar fata ne, amma daga bisani mai bada horon ya ba da hakuri.

Masu bada shawara kan tsaro sun ce kada 'yan wasan su kasance kan titunan birnin, saboda ana ci gaba da zanga-zangar da ake yi wadda ke shafar gasar Nahiyoyin.

Pradelli, kafin wasansu da Brazil ranar Asabar, ya ce duk da cewa ba su da niyyar barin gasar saboda zanga-zangar, amma yana damuwa da yadda lamarin ke dada karuwa.

Karin bayani