Najeriya ta yi asarar Kwallaye—Keshi

Image caption Keshi ya dora alhakkin nasara kan Najeriya da asarar kwallye da suka yi

Mai baiwa tawagar kwallon kafa ta Super Eagles horo, Stephen Keshi, ya ce asarar kwallayen da suka yi a gaban raga ce ta sa aka fitar da Najeriya daga Gasar cin Kofin Nahiyoyi.

Zakarar kwallon kafar ta Afrika ta zama ta kusa da karshe a rukunin ta bayan da Spain ta lallasa ta da ci uku ba ko daya.

Acewar Keshi, "mun ta kirkirar dama mai yawa ta cin kwallo amma dabarbarcewa ta hana mu saka kwallo ko guda daya."

Najeriyar dai na bukatar ta ci wasan Lahadin don ta samu damar shiga zagaye na biyu a gasar amma hakan ba ta samu ba.

Keshi ya kuma koka cewa yawancin 'yan wasan sa maciya kwallo na da rauni ba su buga wasan ba.

Karin bayani