Masar ta fara wasanta da rashin sa'a

Image caption Masar ta faran wasan gasar 'yan kasa da 20 ba nasara

Kasar Masar ta fara wasanta na Gasar cin Kofin Duniya na 'yan kasa da shekaru 20 da rashin sa'a; inda Kasar Chile ta doke ta da ci biyu da daya.

A mintuna goma ne da fara wasan Mahmoud Kahraba na Masar ya zura kwallo.

Chile ta rama a minti na ashirin da biyar inda Nicolas Castillo ya doka kwallon kusa da raga ya farke kwallon.

Sai kuma Christian Bravo wanda ya shigo daga baya ya karawa yawan kwallayen Chile a minti n goma sha hudu da dawowa daga hutun rabin lokaci zagaye na biyu; abinda ya bawa Chilen nasara kan Masar.

Karin bayani