Baletolli ba zai buga karashen wasanni ba

Image caption Balotelli ba zai buga ragowar wasanni ba

Dan wasan gaban nan na Italiya Mario Balotelli, an yi ittifakin ba zai buga sauran wasannin Gasar cin Kofin Nahiyoyi ba saboda rauni da ya ji a cinya.

Tsohon dan gaban Manchester City, Balotelli, mai shekaru 22, ya zura kwallo a wasannin da Italiyar ta yi da Mexico da Japan na rukuni-rukuni a gasar.

Ya buga cikakken wasa na mintuna 90 inda suka ci Brazil 4 da 2 amma ba zai buga wasan kusa da karshe da Spain ba ranar Alhamis.

Likitan tawagar, Enrico Castellacci, ya ce dan wasan ba zai warke ba daga yanzu zuwa ranar Lahadi.

Karin bayani