Brazil za ta dauki nauyin kwallon duniya

Dodon wasan gasar cin kofin kwallon kafa na duniya
Image caption Mutum-mutumin wasan gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da Brazil za ta dauki nauyi a badi

Babban magatakardar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Jerome Valcke yace tabbas Brazil za ta dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekarar 2014.

Ya fadi hakan duk da cewa ya yi tattaunawa da gwamnatin kasar game da ko za a soke gasar nahiyoyi na duniya, saboda zanga-zangar da ake yi a kasar.

Valcke ya amince cewa boren ya dauke hankalin mutane daga gasar, amma ya bada tabbacin cewa kasar zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniyar, bayan ya samu tabbaci daga gwamnati kan tabbatar da kariya.

"Za a yi gasar cin kofin duniya a Brazil" ya shaida wa BBC.

Inda ya kara da cewa "Wasan farko za a yi shi ne a Sao Paulo, na karshe kuma za a buga a Rio, babu wani shirin da ya wuce wannan."

A karshen makon jiya ne dai miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na Brazil suka fantsama kan tituna suna zanga-zanga.

Boren wanda aka yi a kusan birane 100 na kasar ya somo asali ne, saboda karin kudin mota da matsalar cin hanci da rashawa, bugu da kari ga kudaden da kasar za ta kashe wajen daukar nauyi gasar cin kofin duniyar.