An nada Ancelotti manajan Real Madrid

Image caption An nada Carlo Ancelotti manajan Real Madrid

Carlo Ancelotti ya zama manajan kulob din Real Madrid, shi kuma Laurent Blanc ya maye gurbin Ancelottin a Paris St-German.

Ancelotti dan shekaru 54, ya jagoranci PSG a gasar cin kofin Faransa a kakar wasannin da ta gabata amma ya bar kulob din a watan Mayun da ya gabata a lokacin da Real Madrid ta bukace shi.

Ya sanya hannu a kwantiragin shekaru uku a Spain dan maye gurbin Jose Mourinho, wanda ya zama shugaban kulob din Chelsea.

Shi kuwa Blanc dan shekara 47, ya amince da kwantiragin shekaru biyu da PSGn.

Da alama sai da PSG ta samu wanda zai maye gurbin Ancelottikafin su ka kyale shi ya tafi, a don haka suka ce sun yi murna da nada Blanc wanda suke nuna farin cikin nada shi a matsayin shugaban kulob din.

Zai fara aiki daya ga watan Yuli dan fara atisaye kafin fara kakar wasanni.

Blanc ya yi wasa da Montpellier, da Auxerre, da Barcelona, da kuma Manchester United a lokacin da ya ke buga kwallo, yana kuma daga cikin 'yan wasan Faransa da suka ci kofin duniya a shekarar 1998 da kuma Euro 2000.

Karin bayani