Azarenka ta bar gasar Wimbledon

Image caption Azarenka ta bar gasar Wimbledon saboda rauni

Gogaggiyar 'yar wasan kwallon tennis din nan Victoria Azarenka na daya daga cikin 'yan wasanni biyar da suka bar gasar Wimbledon ranar Laraba bayan da bata sami saukin ciwon gwiwa ba.

'Yar wasan ta biyu a duniya wadda ta ci Mario Joao Koehler ta fadi ta fadi sosai a wasan ranar Litinin.

Da farko dai Steve Darcis wanda ya doke Rafael Nadal a zagaye na farko shi ma ya bar gasar saboda matsalar kafadarsa.

Maric Cilic ma ya fita saboda ciwon gwiwa.

Karin bayani