Tevez zai koma Juventus

Image caption Tevez zai koma Juventus

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da Juventus sun cimma daidaito kan siyan dan wasan nan Carlo Tevez, a kan kudi kusan fam miliyan 12.

Dan kasar Argentina, mai shekaru 29 ana tsammanin zai isa Italiya ranar Laraba domin yin gwaje-gwajen lafiyar sa da kuma tattaunawa kan abin da ya shafi rayuwarsa kan kwantaragin shekaru uku.

Kulob din biyu sun cimma yarjejeiyar ne a wani taro da suka yi a London ranar Talata.

Tevez ya rattaba hannu a kwantiragin shekaru biyar, yayin da ya koma Manchester City a shekarar 2009.

Karin bayani