Andrew na Ghana na shagube kan dawowarsa

Image caption Ghana na kokarin fitowa kwallon duniya

Andrew Ayew na kasar Ghana na fatan yunkurin kasar na neman fitowa Gasar cin Kofin Duniya ba zai samu nakasu saboda dawowarsa da dan uwansa Jordan ba.

Yawancin batun da ake yi kan wasan da za su buga da Zambia a watan Satumba ba wai a kan wasan kansa ba ne.

Ana magana ne sosai a kan dawowar wa da kanin daga gudun hijirar da suka yi da kansu.

Rashin jituwa tsakanin su da Kocin tawagar Ghanan Kwesi Appiah ce ta sa Andrew ya bar Black Stars.

Karin bayani