David Moyes ya kama aiki a Man U

Image caption David Moyes ya kama aiki a matsayin Kociyan Man U

David Moyes ya fara sabon aikinsa na kociyan zakarun Premier League, Manchester United a yau Litinin.

Sabon Kociyan mai shekaru 50 ya bar Kulob din Everton ne ya maye gurbin Sir Alex Ferguson, wanda ya yi ritaya a karshen kakar wasanni bayan shekaru 26 ya na jagorancin kulob din a Old Trafford.

Moyes ya tuka kansa zuwa filin wasan United a a safiyar yau Litinin a kudancin Manchester.

Daya daga cikin batutuwan da Moyes, wanda ya sa hannu a kwantaragin shekaru shida zai duba shine batun makomar dan wasannan Wayne Rooney.

Rooney, wanda aka ce ya bar United a watan Octoba na shekara ta 2010, ya yi wasa a karkashin Moyes a Everton kafin ya koma United a watan Agusta na shekara ta 2004, amma ko zai zauna a kulob din ko kuma akasin haka batu ne da lokaci ne zai tabbatar da hakan.

Karin bayani