Habasha ta rasa maki a wasan Botswana

Image caption Habasha ta rasa maki a wasan Botswana

Kasar Ethiopia ta rasa maki saboda saka dan wasan da bai dace ba, a wasan da ta buga da Botswana wanda ta ci nasara da ci biyu da daya.

A wasan na neman fitowa gasar cin kofin Duniya, dan wasan Habashan Minyahil Teshome Beyene bai kamata ya buga wasan ba saboda ya na da yelon kati biyu.

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa ta bawa Bostwana nasara da ci uku ba ko daya.

Wannan ya bawa Bostwana damar samun fitowa gasar cin kofin duniyar.

Hakazalika, an ci tarar Hukumar kwallon kafa ta Habashan dala dubu shida da dari uku saboda keta dokar ladabtarwar ta Fifa.

Karin bayani