Eagles na shirin wasa da Cote 'D Ivoire

Image caption Eagles na shirin wasa da Code 'D Ivoire

Tawagar 'yan wasan Super Eagles kusan sun gama hallara a babban birnin Tarayya Abuja, don shirin buga wasan share fagen wasan duniya da Tawagar 'yan wasan Cote 'D I voire wato Elephants.

A cikin 'yan wasa ashirin da hudu ashirin da daya tuni sun isa kuma sun fara samun horo a filin wasa na Abuja a safiyar yau Litinin.

Sai dai dan wasan kano Pillars da yake tawagar, Umar Zango ba zai iya shiga ba saboda rauni da yake fama da shi wanda yaji a wasan Kulob din sa na Kano Pillars da Dolphins na Port Harcourt.

An gayyato Adamu Murtala zai maye gurbin Umar Zangon.

Karin bayani