Liverpool ta sayi Kolo Toure

Image caption Liverpool ta sayi Kolo Toure

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kammala rattaba hannu a kan kwantaragin dan wasan bayan Manchester City din nan Kolo Toure.

Dan wasan mai shekaru 32, ya je Anfield a kwantaragin shekaru biyu bayan kwantaraginsa a filin wasan Etihad ta kare.

Toure, dan wasan kasar Ivory Coast ya bayyana a wasannin Manchester City 102 bayan da ya koma kulob din daga Arsenal a kan kudi fam miliyan 14 a watan Yuli na shekara ta 2009.

Gogaggen dan wasan dai yana cikin tawagar kulob din da su ka ci kofin Gasar Premier a kakar wasanta 2011/2012.

Karin bayani