Roberto Martinez zai koma Wigan

Image caption Roberto Martinez zai koma Wigan

Sabon mai bada horo na Everton Roberto Martinez zai koma tsohon kulob dinsa Wigan Athletic, zai kuma rattaba hannu a kan kwantaragi na farko na sayan 'yan wasa biyu: Arouna Kone da kuma Antolin Alcaraz.

Tattaunawa tsakanin kulob din biyu kan dan wasan gaban Kone wanda ya zura kwallaye 11 a Gasar Premier a kakar wasannin bara na samun nasara.

Amma Martinez zai duba makomar Leighton Baines yayin da ya fara aiki ranar Laraba.

Manchester United ta yi tayin dan wasan bayan na Ingila amma Everton ta ki amincewa sai dai sabon Kociyan David Moyes zai iya ba da wani tayin mai tsoka.

Karin bayani