'Rooney na bukatar barin Man U'

Wayne Rooney
Image caption Phelan na ganin Rooney na da karin rawar da zai taka a Manchester United

Tsohon mataimakin manajan kulob din Manchester United, Mike Phelan ya ce dan wasan gaba Wayne Rooney na bukatar ya bar Manchester United.

Rooney mai shekaru 27, acewar rahotanni ya nemi ya bar kulob din a karshen kakar wasannin da ta gabata, karo na biyu kenan na bukatar hakan a cikin shekaru uku.

Phelan ya shaida wa shirin turanci na BBC cewa "Wayne na kulob din da ya fi kowanne, to me zai sa ya so bari, sai dai idan yana son sauyi, kuma ya ga baya samun biyan wata bukata daga Manchester United."

A watan Oktobar shekarar 2010 ma, Rooney ya so ya bar Man U inda aka ce yana son komawa Paris St. German a watan Aprilu.

A baya-bayan nan dai akwai rahotannin dake nuna cewa kulob din Arsenal da na Chelsea sun nuna sha'awarsu ga dan wasan.

A wannan makon ne dan wasan Ingilan zai gana da manajan kulob din Man U, David Moyes domin tattaunawa a kan makomarsa.