Stephen Keshi zai tattauna da Anichebe

Stephen Keshi
Image caption Stephen Keshi na kewar Victor Anichebe

Mai horar da 'yan wasan Najeriya Stephen Keshi yana son tattaunawa tare da Victor Anichebe game da kasancewar sa a cikin 'yan wasan dake bugawa Najeriyar tamaula

Keshi dai na fatan ya rarrashi dan wasan gaban na Everton mai shekaru 25 a duniya domin ya canza ra'ayinsa bayan daya dakatar da buga tamaula a kwanan nan

Keshi dai ya fadawa BBC cewa Anichebe dan wasan gaba ne mai kyau kuma matashi kakkarfa, kuma yace yana fatan kai masa ziyara a Ingila ya kuma yi magana da shi ido da ido

Mai horar da 'yan wasan na Najeriya Stephen Keshi yace yana bukatar goyan bayan hukumar Kwallon kafa ta Najeriya domin ganin cewa Anichebe ya canza ra'ayinsa ba tare da wani bata lokaci ba, saboda a cewar sa ba zasu zura ido suyi asarar dan wasan ba.

Karin bayani