Uruguay ta lallasa Najeriya 2-1

Wani dan kwallon Najeriya na gara kwallo
Image caption Wani dan kwallon Najeriya na gara kwallo

Kungiyar kwallon kafa ta Uruguay ta doke takwararta ta Najeriya da ci 2-1, a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na 'yan kasa da shekaru 20.

Hakan dai ya kawar da fatan da Najeriyar keyi na daukar kofin gasar da ake yi a kasar Turkiyya.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci ne a taka ledar, 'yan wasan Flying Eagles suka koma 10, bayan an baiwa Abdullahi Shehu jan kati a mintoci 41 da fara wasan.

Nicolas Lopez ne ya zura wa Uruguay kwallaye biyu a ragar Najeriya, har da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Yayin da Olarenwaju Kayode ya farke wa Najeriya kwallo daya.

A halin yanzu dai Ghana ita ce kasar Afrikan da ta rage a gasar, kuma za ta kara da Portugal a ranar Laraba.

Mali da mai rike da kambun Afrika, wato Masar basu kai labari ba, inda aka fitar da su tun a wasannin rukuni-rukuni.