Giggs zai horar da 'yan wasan Man Utd

Ryan Giggs da Phil Neville
Image caption Ryan Giggs da Phil Neville

Kulob din kwallon kafa na Manchester United ya ayyana sunayen 'yan wasansa Ryan Giggs da Phil Neville a matsayin wadanda za su shiga sahun masu horar da 'yan wasan kulob din.

Ryan Giggs da takwararsa Neville su ne na baya-bayan nan da aka bai wa mukamin masu horar da 'yan wasa, karkashin jagorancin Kociyan kulob din, David Moyes.

Moyes ya ce "Na ji dadi da Ryan Giggs ya amince da kasancewa dan wasa kuma mai taimaka wa wajen horar da 'yan wasa."

Shi ma Ryan Giggs ya bayyana nadin nasa da cewa wani matakin farko ne game da makomar rayuwarsa.

Giggs, wanda a watan Nuwamba mai zuwa zai cika shekara 40 da haihuwa, ya taka leda wa kulab din Manchester United a wasanni daban-daban sau 941, inda ya jefa kwallaye 168 a raga.

Kuma da shi kulob din ya ci gasar Premier har sau 13 da gasar zakaraun Turai hudu da kofin FA hudu da kuma kofin League kuma hudu.