Manchester City na zawarcin Negrado

Alvaro Negredo
Image caption Alvaro Negredo

Kulob din Manchester City ya nuna sha'awar sayen dan wasan gaba na kulob din Sevilla na kasar Spain, Alvaro Negredo da ake wa tsammanin farashinsa zai kai Fam miliyan 24.

Ko da yake kulob din Man City na tsammanin samun ragi.

Manchester City dai na so Alvaro Negredo ya maye gurbin Carlos Tevez, bayan komawarsa kulob din Juventus.

Kulob din Atletico Madrid na daga cikin wadanda suka yi yunkurin sayen Negredo, amma sabon Kociyan City, Manuel Pellegrini ya bayyana cewa Negrado ne zai iya maye gurbin Tevez.

Kulob din Everton da West Ham su ma sun yi sha'awar sayen dan wasan, amma tsada ta kore su.