Murray ya lashe gasar Wimbledon

Andy Murray
Image caption Andy Murray ya doke Novak Djokovic a wasan karshe

A cikin shekaru 77 akaron farko, dan wasan Tenis din nan na Burtaniya Andy Murray ya zama zakaran wasan Tenis din Wimbledon a bangaren maza, bayan da ya doke abokin karawarsa Novak Jokovik na Sebia.

A bara dai Roger Federer ya doke shi a wasan karshen.

A ranar asabar kuma Marion Bartoli ta Faransa ta zamo gwarziya ta bangaren mata, bayan data doke Sabine Leziki ta Jamus

And Murray dai ya bayyana faricikinsa kuma ya bayyana cewar nasarar daya samu tazo masa ta bazata, kuma ya bayyana wasan da cewar mai zafi ne.

Shima dai Novak Jokovik ya taya Andy Murray murna

Karin bayani