A bar Rooney ya fayyace makomarsa —Ferdinand

Image caption Ferdinand ya ce Rooney zai iya fuskantar koma-baya

Rio Ferdinand ya ce Wayne Rooney na da cikakken hankalin da zai iya fayyace makomarsa a harkar wasanni, sai dai ya gargade shi cewa idan ya bar United zai iya fuskantar koma-baya a fagen tamaula.

United sun ki amincewa da bukatar Rooney, mai shekaru 27 a duniya, don komawa wani kulob din, kuma sabon kocin kungiyar, David Moyes, ya jaddada cewa ba za su sayar da shi ba.

Ferdinand ya bayar da misalin abin da ya faru ga Cristiano Ronaldo, wanda bai samu nasarorin da Rooney ya samu ba tun lokacin da ya bar Old Trafford ya koma Real Madrid a shekarar 2009.

A cewar Ferdinand, "Ban ga kungiyar da [Rooney ] zai je fiye da nan [United ] ba''.

Ronaldo, mai shekaru 28 a duniya, ya zura kwallaye 193 a wasanni 207 da ya buga tun lokacin da ya koma Real Madrid, amma ya ci gasar La Liga sau daya kawai, sannan ya ci Copa Del Rey a kakar wasanni hudu a Bernabeu.

Karin bayani