Suarez na son barin Liverpool

Luis Suarez
Image caption Liverpool ta yi watsi da tayin sayen Suarez da Arsenel ta yi, kan kudi fam miliyan 30

Wakilin Luis Suarez ya jaddada cewa dan wasan dan kasar Uruguay, na son ya buga wa wani kulob din dake gasar zakaru wasa.

Ya fadi hakan ne a lokacin tattauna wa da shugaban Liverpool Brender Rodgers da kuma babban daraktan kulob din Ian Ayre.

Wakilin, Pere Guadiola ya gana da jami'an ne a lokuta daban- daban, ganawar da suka gudana lami-lafiya.

Liverpool dai ta dage cewa ba ta sauya matsayi game da Suarez ba, kuma ta na son ci gaba da rike dan wasan mai shekaru 26, yayin da Guardiola kuma bai mika takardar neman barin kulob din a madadin Suarez ba.

A halin yanzu dai Suarez na hutu bayan buga wa kasarsa Uruguay wasa a gasar cin kofin nahiyoyin da aka kammala a Brazil.