Ghana ta shirya tunkarar Faransa

'Yan wasan kasar Ghana
Image caption 'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Ghana

Mai horar da 'yan wasan Ghana, Sellas Tetteh na da kwarin gwiwa cewa kungiyarsa za ta doke ta Faransa, a zagayen kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 20.

Za dai ayi taka ledar tsakanin kasashen biyu a ranar Laraba.

Sai dai Ghanar za ta yi wasa ne ba tare da 'yan wasa uku ba a zagayen na kusa da na karshen.

'Yan wasan da aka dakatar nata sun hada da dan wasan tsakiya, Moses Odjer da kuma 'yan wasan baya Joseph Attamah da Lawrence Lartey.

Tetteh ya fadi hakan, duk da cewa an doke Ghanar a gasar rukunin A, lokacin da aka bude gasar.

Doke Ghanar da ci 3-1 da aka yi shi ne karo na farko da kasar ta sha kaye a wasannin rukuni-rukuni, a wasanni shida da ta yi a gasar.

Haka kuma Spaniya ma ta doke Ghanar da ci daya da nema, amma Ghana ta doke Amurka da Koriya ta Kudu, inda ta samu shiga kungiyoyi 16 da suka rage, kafin ta zo ta doke Portugal da ci 3-2.

Tetteh ya yi amanna cewa 'yan wasansa na samu karin kuzari, yayin da ake cigaba da gasar a Turkiyya, kuma a wannan karon za su lallasa Fransa.