Leonardo yana shirin barin PSG

Image caption An dakatar da Leonardo har tsawon watanni 13

Leonardo ya ajiye mukaminsa na daraktan wasanni a kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain kuma yana shirin barin kungiyar a karshen watan Agusta.

An dakatar da tsohon dan wasan na gaba na Brazil mai shekaru 43 a duniya, daga shiga harkokin wasanni na tsawon watanni tara saboda ya ture alkalin wasa a watan Mayu.

Daga bisani an tsawaita dakatarwar zuwa watanni 13, lamarin da ke nufin ba zai shiga harkokin wasanni ba a kakar wasanni mai zuwa.

Wannan mataki ne dai ya sanya shi barin kungiyar.

A cewar PSG : "Ba mu ji dadin wannan mataki da ya dauka ba, amma za mu mutunta wannan shawara da ya yanke. Don haka muna yi masa fatan alheri''.

An nuna hoton Leonardo yana hankade alkalin wasa Alexandre Castro a kan hanyarsu ta zuwa dakin da 'yan wasa ke hutu, a lokacin wasansu da suka yi kunnen-doki da Valenciennes.

Karin bayani