U20: Faransa ta doke Ghana, 2 - 1

'Yan wasan kwallon Ghana
Image caption 'Yan wasan kwallon Ghana

Kungiyar kwallon kafa ta Faransa ta doke takwararta ta Ghana da ci 2 da 1, a zagayen kusa da karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na 'yan kasa da shekaru 20.

Rashin samun nasarar kungiyar Ghana ta Black Satllites, ya biyo bayan kwallon da dan wasan Faransa Florian Thauvin ya zura sau biyu, kafin hutun rabin lokaci da kuma bayan an dawo.

Ebenezer Assifuah shi ne ya farke wa Ghana kwallo daya.

Faransa ta samu nasara a gasar duk da cewa an kori dan wasan bayanta Samuel Umtiti, a sulusin karshe na taka ledar.

Wannan ne dai karon farko da kungiyar Faransa ta kai labari zuwa zagayen karshe, tun bayan da ta zamo kasar nahiyar Turai ta farko da ta taba daukar kofin, bayan Spaniya a shekarar 1999.

Ghana dai ta taba lashe gasar 'yan kasa da shekaru 20 din, bayan doke Brazil a shekarar 2009.