Ana bincike kan sayar da wasa a Spain

Image caption Racing Santander sun ce ba su aikata wani laifi ba

Hukumar da ke kula da Gasar La Liga ta Spain ta ce tana gudanar da bincike domin gano ko an sayar da wasa ne a wasan da Racing Santander ta doke Hercules da ci uku ba ko daya, wanda aka yi ranar 8 ga watan Yuni.

Kakakin hukumar, Juan Carlos Santamaria, ya ce sun kaddamar da binciken ne a ranar 3 ga wannan watan, bayan hukumar ta karbi wani rahoto da ke zargin cewa an sayar da wasan tun kafin a buga shi.

Santander dai sun musanta zargin, suna masu cewa kwarewar 'yan wasansu ce ta sanya suka yi nasara.

Duk da lashe wasan na rukuni na biyu da Santander suka yi ba su kai labari a rukunin ba.

Karin bayani