Swansea ta sayi Wilfried Bony

Image caption Bony ba zai koma Swansea ba sai ya samu izinin yin aiki a Burtaniya

Kungiyar kwallon kafa ta Swansea City ta sayi dan wasan Vitesse Arnhem, Wilfried Bony, a kan kudi fam miliyan 12, sai dai ba zai koma kungiyar ba sai ya samu izinin yin aiki a Burtaniya.

Bony, wanda ya sanya hannu a kwantiragin shekaru hudu da kungiyar, ya zura kwallaye 31 a wasanni 30 da aka sanya shi a kakar wasan da ta wuce.

Kungiyar West Ham ma ta so sayen dan wasan mai shekaru 24 dan kasar Ivory Coast, amma Swansea ta yi nasara bayan ta saye shi a kan kudin da ya fi wanda West Ham ta so sayensa.

A cewarsa: "Na dade ina son yin wasa a Gasar Premier."

Bony shi ne dan wasa na bakwai da ya koma Swansea a kakar wasa ta bana.

Sauran 'yan wasan da Swansea ta saya su ne: Jonjo Shelvey daga Liverpool, Alejandro Pozuelo da Jose Canas daga Real Betis, Jordi Amat daga Espanyol, Gregor Zabret daga NK Domzale da kuma Alex Gogic wanda ta sayo daga Olympiakos.

Karin bayani