Liverpool ta karawa Gerrard shekaru 2

steven gerrard
Image caption Steven Gerrard zai ci gaba da zama a Liverpool har ya cika shekaru 35

Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard zai kara tsawon kwantiraginsa da shekaru biyu nan da gobe Talata.

Tun a karshen kakar wasannin da ta kare ne a ke tattaunawa tsakanin wakilin Gerrard da manajan daraktan klub din Ian Ayre kan ci gaba da zamansa a kungiyar.

Duk da cewa dan wasan bai samu damar yin wasannin karshe na kungiyar na karshen kakar wasannin ta bara ba saboda aikin da aka yi masa a kafada, kungiyar ta gamsu da lafiyarsa a yanzu.

A karshen kakar wasanni mai zuwa kwantiraginsa da klub din zai kare amma kociyansu Brendan Rodgers, ya bukaci ci gaba da zaman dan wasan mai shekaru 33 na wasu shekaru biyu.

A ranar Litinin dinnan kungiyar ta Liverpool za ta tafi rangadin wasannin shirin tunkurar kaka mai zuwa a Australia da Asia.

A ranar 29 ga watan Nuwamba na 1998, Gerrard ya fara bugawa Liverpool wasan farko da Blackburn Rovers.

A 2003 ne Gerrard ya gaji Sami Hyypia a matsayin kyaftin a klub din.

Kuma shi ne ya zama dan wasan da ya fi ci musu kwallo a kakar wasanni ta 2004-05 da 2005-6 da kuma 2008-09, inda ya ci wa klub din kwallaye 159 a wasanni 630 na manya.

Kofunan da ya dauka da kungiyar sun hada da na Zakarun Turai daya da na Uefa daya da na FA biyu da kofin kalubale 3. Sauran sun hada da kofin Community Shield guda biyu da kuma Super Cup na Turai biyu.

A shekara ta 2005, Gerrard ya bukaci Liverpool ta bashi dama ya koma Chelsea inda daga baya ya sauya shawara.