Paris Saint-Germain ta sayi Cavani

edinson cavani
Image caption Sayen Edison Cavani da kungiyar PSG ta yi ta dara mai hamayya da ita Monaco

Paris Saint-Germain ta sayi Edinson Cavani mai shekaru 26 a kan euro miliyan 64 daga Napoli, sama da mako daya bayan da klub din ya bayyana cewa gab ya ke da kammala cinikin.

Hakan ta tabbata ne bayan da kungiyar Monaco da ke hamayya da PSG din ta sayi Radamel Falcao daga Atletico Madrid a kan euro miliyan 60.

Bayan kuma daman kungiyar ta Monacon ta sayi James Rodriguez a euro miliyan 45.

A ranar Litinin ne Cavani dan kasar Uruguay ya je Paris inda klub din ya duba lafiyarsa.

A ranar Talatar nan ake saran shugaban klub din Nasser Al Khelaifi zai gabatar da dan wasan ga 'yan jarida.

Shi kuwa Leonardo ya shedawa kungiyar ta PSG cewa a karshen lokacin musayar 'yan wasa ranar biyu ga watan Satumba zai bar klub din.