Fabregas ba ya son barin Barca- Vilanova

cesc fabregas
Image caption Cesc Fabregas ya kasance daya daga cikin manyan 'yan wasan Arsenal karkashin Wenger

Kociyan Barcelona Tito Vilanova ya ce Cesc Fabregas yana son ci gaba da zama a kungiyar.

Ba ya son komawa gasar Premier a bana, bayan tayin da Manchester United ta yi na sayensa.

A ranar Litinin ne Manchester United ta taya tsohon kyaftin din Arsenal din mai shekaru 26 fam miliyan 25 amma dan wasan ya ce shi dai a yanzu yana son ci gaba da zama a Barca.

Vilanova ya ce dan wasan dan kasar Spaniya ya sheda masa cewa burinsa ne ya ci gaba da zama a Barcelona.

Kociyan ya kara da cewa, fabregas ya ce ba ya son tafiya wata kungiya saboda kudi ko kuma don a rika sanya shi a wasa kawai.

Har zuwa yanzu dai Barcelona ba ta ba wa Man United amsa a dangane da tayin sayen dan wasan da ta yi ba, farashin da ake gani bai kai kimar da Barcelona ta yi masa ba.