Kofin Europa abin kunya ne- Mourinho

jose mourinho
Image caption Mourinho ya ce kofin Zakarun Turai da na Premier su ne burinsa a Chelsea bana

Jose Mourinho ya ce kofin Europa da Chelsea ta dauka ba wani abin alfahari ba ne, Kuma da a lokacinsa ta dauka da zai zama babban abin kunya a gare shi.

A kakar wasannin da ta wuce ne Chelsea ta dauki kofin na Europa, bayan an fitar da ita daga gasar Zakarun Turai a wasannin rukuni.

Amma kuma ta kai ga daukar kofin na Europa bayan ta yi galaba akan Benfica a watan Mayu.

Mourinho, ya ce, ''ba na son 'yan wasana su dauka cewa gasar Europa tamu ce.''

Kociyan wanda ya jagoranci Porto ta dauki kofin Zakarun Turai a 2004, ya kuma dauka da Inter Milan a 2010, ya ce, a bana ma kofin da na Premier su ne burinsa.

Ya ce, '' Chelsea tana neman kofin na Zakarun Turai na biyu, ni kuma ina neman na uku, za mu yi kokarin cimma wannan buri.''

Tsohon kociyan na Real madrid wanda ya sake dawowa Chelsea a karo na biyu ya ce ba ruwansa da batun wani dan wasa fitacce, idan zai yi zabe

dole ne kowa ya yi kwazo kafin ya sa shi a wasa.

Game da tsofaffin 'yan wasa irin su John Terry mai shekaru 32 da Frank Lampard mai shekara 35, ya ce bai damu da yawan shekarun 'yan wasa ba, idan sun fi matasa kwazo su zai yi amfani da su idan kuma matasan ne suka fi su zai sa.