Man U ta ki tayin Chelsea na Rooney

wayne rooney
Image caption Rooney ya ce bai yarda ya yi zaman jiran ko-ta-kwana a kan Van Persie ba

Manchester United ta yi watsi da bukatar Chelsea ta sayen Wayne Rooney,inda ta kara nanata cewa dan wasan ba na sayarwa ba ne.

Kugiyar Chelsea wadda ta tabbatar tana neman dan wasan ta musanta cewa za ta bada kudi da wani daga cikin 'yan wasanta Juan Mata ko kuma David Luiz a kansa.

Duk da cewa dai Manchester United ta ki amsa bukatar ana ganin Chelsea za ta sake tayi da karin kudi.

Rooney ya kara bayyana aniyarsa ta barin klub din bayan da kociyan Manchester United din David Moyes ya ce dan wasan zai rika zaman jiran ko-ta-kwana ne, idan Van Persie ya ji rauni ko wata matsala a sa shi.

Hakan ya sa Rooneyn shi kuma ya ce ba za ta sabu ba ya yi zaman ko-ta-kwana a kungiyar.

Daga nan ne kuma mai horadda 'yan wasan Chelsea Jose Mourinho ya fito fili ya nuna sha'awarsa ta sayen dan wasan a wata hira da BBC a Bangkok ranar Talata.

Chelsea dai ta nuna rashin jin dadinta na bayyanar labarin cewa ta nemi dan wasan, inda ta ce lalle hakan ne amma babu maganar ba da kudi da wani dan wasanta a cinikin, wanda ba a bayyana yawan kudin ba.