Cisse ya yi watsi da Newcastle

papiss cisse
Image caption Cisse wanda ya koma Necastle a watan Janairu na 2012 ya ci kwallaye 26

Dan wasan Newcastle Papiss Cisse ya ki bin tawagar kungiyar rangadin wasannin share fagen kakar wasanni mai zuwa a Portugal a kan akidar addini.

Dan wasan wanda musulmi ne ya ce ba zai sa rigar wasan kungiyar mai dauke da tambarin kamfanin Wonga wanda shi ne sabon kamfanin da kungiyar ta kulla yarjejeniya da shi ta daukar nauyin rigar ba.

Cisse ya bijire ne akan cewa kamfanin mai bada rancen kudi yana cin riba ta hanyar tsauwala kudin ruwa a basukan da yake bayarwa.

Saboda haka ya ce shi kam ba zai tallata wanna kamfani ba.

Dan wasan dan kasar Senegal mai shekaru 28, a maimakon rigar ya ce zai sa wadda ba ta dauke da tambarin kamfanin ko kuma wata mai dauke da tambarin wata kungiya mai bada agaji.

Tattaunawar da aka yi ta yi tsakanin wakilin dan wasan da klub din da kuma kungiyar kwararrun 'yan wasa ta Ingila domin sasanta matsalar ta ci tura.

Lamarin da ya sa ake ganin ci gaba da zaman dan wasan a kungiyar zai yi wuya, saboda ya nuna cewa ba gudu ba ja da baya akan matsayinsa.

Sai dai kuma abokan wasan Cisse a klub din Cheick Tiote da Moussa Sissoko wadanda dukkanninsu musulmai ne suma, sun ce ba su da wata matsala dangane da sanya rigar (jesin).