Keshi ya gayyaci 'yan wasa ashirin

stephen keshi
Image caption Galibin 'yan wasan da Keshi ya gayyata wadanda suka je gasar Zakarun nahiyoyi a Brazil ne

Kociyan Super Eagles na Najeriya Stephen Keshi ya gayyaci 'yan wasa 20 domin gagarumin wasan sada zumuntar da za a yi tsakaninsu da Afrika ta Kudu a birnin Durban na Afrika ta Kudun ranar 14 ga watan Agusta.

Wasan da ake wa lakabi da Gasar Mandela da a ke yi shekara shekara ana yi ne domin martaba tsohon shugaban kasar ta Afrika ta Kudu wanda yanzu ya ke fama da rashin lafiya.

'yan wasan da kocin na Najeriya ya gayyata sun hada da Emmanuel Emenike wanda ke wasa a Rasha, da kuma shi ne ya fi zura kwallaye a raga a gasar cin Kofin Afrika da Najeriyar ta dauka a Afrika ta Kudu a farkon shekarar nan.

Dan wasan zai sake dawowa cikin tawagar 'yan wasan Najeriyar a karon farko tun bayan wannan gasa.

Haka shi ma dan wasan Newcastle United Shola Ameobi, wanda a kwanakin nan ya samu kansa daga tarnakin da ya hana shi yi wa Najeriya wasa ya samu goron gayyata.

Dan wasan gaba na Chelsea da ya yi jiyya a kwanakin nan Victor Moses shi ma ya dawo, amma kuma mai tsaron gida kuma kyaftin din 'yan wasan na najeriya Vincent Enyeama baya cikin tawagar.

Obinna Nsofor ya dawo cikin tawagar bayan shekaru biyu ba a ji duriyarsa ba a kasashen waje.

Tsohon dan wasan Najeriya na kungiyar matasa Uche Nwofor na klub din VVV Venlo da ke Netherlands ba tsammani an sa shi cikin tawagar, wadda galibi 'yan wasan da suka je gasar Kofin Zakarun Nahiyoyi suka mamaye.

Kociyan na najeriya ya kuma ajiye 'yan wasa uku na cikin gida, Benjamin Francis da Solomon Kwambe da kuma Muhammad Gambo a zaman ko-ta-kwana da kuma Samuel Aaron da ke wasa a Norway wanda ba a san shi ba sosai.