Mourinho ya gargadi 'yan wasa

jose mourinho
Image caption An hana Mourinho magana a game da sayen Wayne Rooney

Mourinho ya gargadi 'yan wasa cewa kasancewarsu na biyu a kungiyoyinsu maimakon 'yan wasan farko ka iya kawo musu cikas wajen samun damar wasa a gasar Kofin Duniya mai zuwa.

Kociyan na Chelsea ya bayyana hakan ne bayan da Manchester United ta ki tayin sayen Wayne Rooney da kungiyarsa ta yi.

Rooney mai shekaru 27 ya harzuka bayan da kociyan Manchester United din David Moyes ya ce zai rika zaman jiran ko-ta-kwana ne na Robin van Persie.

Mourinho ya ce kafin a dauki dan wasa ya je wa kasarsa gasar Kofin Duniya galibi sai ya kasance daya daga cikin na farko a kungiyarsa.

Kociyan na Chelsea ya yi wadannan kalamai ne a Kuala Lumpur, inda jami'an klub din suka ce ba zai yi magana ba a kan yunkurinsu na sayen Rooney da ya ci tura.

Mourinho ya kara da dewa duk wani dan wasa da ya ke son zuwa gasar Kofin Duniya kuma kungiyarsa, ba ta sa shi a wasa a kai a kai to ba shakka yana cikin matsala.