Fifa da Uefa sun yi rashin nasara

brazil england
Image caption Za a ci gaba da kallon duk wasannin Kofin Duniya a Birtaniya kyauta

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa da ta Turai Uefa sun yi rashin nasara a daukaka karar da suka yi ta neman hana nuna wasannin Kofin Duniya da na Turai a talabijin kyauta a Birtaniya.

Hukumomin biyu sun daukaka karar ne bayan da Babbar kotun Turai a 2011 ta yanke hukuncin cewa Birtaniya za ta iya sanya wasannin biyu a jerin wadanda a ke iya gani kyauta domin amfanin jama'a.

Bayan hakan ne kuma sai Fifa da Uefan suka daukaka kara a kotun koli ta Turai cewa hukuncin zai hana su sayar da damar nuna wasannin ga gidajen talabijin a ainahin kimarsu.

Amma kuma kotun kolin yanzu ta zartar cewa hukuncin da Babbar kotun ta yi a baya daidai ne.

Saboda kamar yadda Birtaniyan ta ce wasannin biyu wasu bangarori ne na muhimman wasannin kasa da ya wajaba a bari kowa ya kalla a talabijin kyauta..

Wanda kuma idan aka ce sai a tashoshin talabijin na kudi za a nuna za a hana mutane da dama damar kallon wasannin.

Karin bayani