Golf: Phil Mickelson ya dauki kofi

phil mickelson
Image caption Mickelson ya zama dan golf na uku a jere mai shekaru 40 da suka dauki kofin gasar ta Muirfield

Phil Mickelson ya zama zakaran gasar kwallon golf ta 2013 ta Muirfield.

Mickelson ba Amurke mai shekaru 43 ya taso daga baya ne ya yi nasarar a kan Henrik Stenson na Sweden.

Da 'yan wasan Birtaniya biyu Ian Poulter da Lee Westwood da kuma zakaran gasar Australia Adam Scott.

Na daya a wasan na golf a duniya, Tiger Woods, yana bayan Westwood na Birtaniya. Inda ya ke harin daukar kofi na 15 na wata babbar gasa kuma na farko tun 2008.

Amma kuma ya samju koma baya, da daman ba ya wani abin a-zo-a-gani a gasar ta Murifield.