Manchester United ta kara taya Fabregas

cesc fabregas
Image caption Ba safai Barcelona ta ke sa Cesc Fabregas a tsakiya ba inda ya fi so.

Manchester United ta kara kudin tayin Cesc Fabregas na Barcelona zuwa fam miliyan 30.

Har yanzu dai ba a ji ta bakin Barcelona a kan sabon tayin ba, amma ana ganin murabus din da mai horad da 'yan wasan Barcelonan ya yi ke kara tsaurara al'amarin.

Shi dai kociyan na Barcelona Tito Vilanova ya snar da saukar sa daga aikin ne sakamakon rashin lafiyar cutar daji da ya ke fama da shi.

Ba a dai san ko neman da Chelsea ta ke yi wa Rooney na da nasaba da bukatar Fabregas da Man United ke yi ba.

Man United dai ta tabbatar da tayin Fabregas din a kan fam miliyan 25 ranar Litinin kuma a yanzu ta kara zuwa fam miliyan 30.

Baya ga Fabregas akwai kuma rahotannin da ke nuni da cewa Man United tana neman Cristiano Ronaldo da Gareth Bale na Tottenham.

Karin bayani